Yanzu Yanzu: Ministan Kimiyya Da Fasaha Yayi Murabus Sakamakon Takardun Karatun Bogi

IMG 20251007 WA0029

Daga Aminu Bala Madobi

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Bayo Onanuga ya tabbatar ga manema labarai cewar ministan kere-kere, kimiyya da fasaha Uche Nnaji ya yi murabus.

A halin da ake ciki yanzu Minista Nnaji Mai Murabus na cikin tsaka mai wuya bayan bankado shedar karatun digiri na karya a Jami’ar Nsukka dake Enugu.

Wannan na zuwane bayan bincike da PREMIUM TIMES ta yi, Jami’ar Nsukka dake Enugu (UNN) ta Najeriya ta yi watsi da takardar shaidar kammala karatun digiri dake hannun tsohon Ministan, inda ta ce dan siyasar bai kammala karatunsa a makarantar ba, kuma ba a taba ba shi satifiket ba.

Kamar yadda bincike na nuna, Simon U. Ortuanya, Shugaban Jam’iar ya bayyana cewa duk da cewa Nnaji ya shiga makarantar a shekarar 1981, amma bai kammala karatunsa ba, kuma be kammala karatun digirin ba.

Binciken ya kara da cewa hukumomi hukumar masu yi wa kasa hidima (NYSC) sun kuma tabbatar da cewa takardar shaidar yi wa kasa hidima da Nnaji ke da ita ba za a iya tantance ta ba.

“Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da murabus din Geoffrey Uche Nnaji, ministan kere-kere, kimiyya da fasaha, biyo bayan wasu zarge-zarge da ake masa.

“Shugaba Tinubu ya nada Nnaji ne a watan Agusta 2023. Ya yi murabus a yau a cikin wata wasika da ya aike da godiyarsa ga shugaban kasa kan yadda ya bashi damar yiwa Najeriya hidima.

“Nnaji ya ce abokan hamayyar siyasar sa ne suka yi masa zagon kasa..

Sanarwar Onanuga ta ce “Shugaba Tinubu ya gode masa saboda hidimar da ya yi kuma ya yi masa fatan alheri a cikin ayyukan da zai yi a nan gaba.”

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *