Daga Aminu Bala Madobi
….Trump ya bukaci firaministan Birtaniya, Keir Starmer, da ya shawarci shugaban Najeriyar da ya dawo gida cikin gaggawa domin tunkarar matsalar tsaro.
Shugaban ƙasar Amurka, Donald J. Trump, ya bayyana halin da kasar Najeriya ke ciki a matsayin babban bala’i, bayan rahotannin hare-haren kunar bakin wake da suka afku a Maiduguri. Ya ce hare-haren sun shafi muhimman wurare kamar asibiti, kasuwa da ofishin waya, guraren cincirindon jama’a lamarin da ya jawo asarar rayukan mutane da marasa laifi.
A cikin sakon na sa, Trump ya soki yadda ake tafiyar da al’amuran tsaro a Najeriya, yana mai cewa rashin tsayayyen shugabanci da raunin kula da iyakoki na daga cikin matsalolin da suka haddasa irin waɗannan hare-hare. Har ila yau, Trump ya nuna damuwa kan rahotannin cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, yana wata ziyara a ƙasar Birtaniya a daidai lokacin da ake fuskantar wannan matsanancin hali.
Shugaban Amurkan ya bukaci firaministan Birtaniya, Keir Starmer, da ya shawarci shugaban Najeriyar da ya dawo gida cikin gaggawa domin tunkarar matsalar tsaro. Ya jaddada cewa jagora nagari ya kamata ya kasance kusa da al’ummarsa a lokacin da suke fuskantar ƙalubale, yana mai kira ga gwamnati ta mayar da hankali kan tsaro da kare rayukan ‘yan ƙasa fiye da komai.
Kalaman shugaban Trump, ya tayar da kura bayan ya bayyana halin tsaro a Najeriya a matsayin abin damuwa, yana mai danganta hare-haren Maiduguri da raunin shugabanci.
Shugaba Donald Trump’ ya nuna damuwa matuka kan rahotannin hare-haren da suka shafi wurare masu muhimmanci tare da asarar rayuka, yana mai kira da a dauki matakan gaggawa domin kare al’umma. Haka kuma ya bukaci firaministan Birtaniya, Keir Starmer, da ya ja hankalin shugaban Najeriya kan muhimmancin kasancewa a gida domin fuskantar ƙalubalen tsaro da ke addabar ƙasar.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t