Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewar Iran ta yi nasarar lalata akasarin sansanonin sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya sakamakon yaƙin da ake gwabzawa tsakanin Iran da Amurka da kuma Isra’ila.
Binciken da kafar talabijin ta CNN ta gudanar ta ce aƙalla sansanoni 16 suka lalace sakamakon harin da Iran ta kai da linzami mai cin dogon zango a yankin.
Bayanai sun ce lalacewar da wasu sansanonin suka yi ya kai mizanin da ba za su iya ci gaba da gudanar da ayyukan da aka kafa su su yi ba.
Binciken ya ce hare haren sun lalata kayan aikin sojin da na sadarwa da kuma matsugunan da sojojn suka zama, abinda ya tilasta sauyawa wasu daga cikin sojojin wurin zama.
Wasu masana sun ce ƙimar adadin ta’adin da hare haren suka yi yayi girma sosai saboda lalacewar kayan aikin sojin da aka gani, wanda ya zarce ƙiyasin da hukumomin Amurka suka yi.
Hukumomin Amurka na cewa ta’adin da hare haren sojin Iran suka kai bai yi tasiri sosai a kan sansanonin Amurkar ba, amma kuma wannan bincike ya nuna cewar ba haka abin ya ke ba.
Binciken da kafar talabijin na NBC ya gudanar ya ce gwamnatin shugaba Donald Trump ta buƙaci kamfanonin sadarwar dake amfani da tauraron ɗan Adam da su daina raba hotunan sansanonin sojin dake Gabas ta Tsakiya.
Rahotan binciken ya ce ko ƴan majalisun Amurka ba su samu cikakken bayani a kan irin ta’adin da hare haren da Iran ta kai da makamai masu linzami suka yi ba, yayin da gwamnati ke neman ƙarin kuɗaɗe domin zuba su a yaƙin da yanzu haka aka tsagaita wuta.
RFI Hausa
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t