A zaɓen 2023, rahotanni sun nuna cewa sai da sa hannun Abdullahi Adamu Shugaban Jam’iyyar APC Na lokacin ya taimaka wajen ceto Sanata Barau Jibrin daga matsin lambar siyasar tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, musamman a lokacin da Ganduje ya riga ya mallaki tikitin Sanatan Kano ta Arewa.
Yayin da ake tunkarar zaɓen 2027, alamu na nuna cewa Barau ya fara ɗaukar matsayi mai tsauri a kan manyan abokan siyasar Ganduje. Ana zargin cewa cire Abdullahi Tijjani Gwarzo daga mukaminsa na minista na da alaƙa da tasirin Barau, kodayake babu tabbaci a hukumance. Haka kuma, a batun zaɓen Mataimakin Gwamna Sule Garo, an ce Barau ya nuna rashin amincewa matuƙa.
A halin yanzu, ana rade-radin cewa shirye-shiryen sasanta ‘yan takarar jam’iyyar APC suna gudana ne ƙarƙashin kulawar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, tare da mai ba shugaban ƙasa shawara Ibrahim Masari, yayin da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke waje.
A wannan mataki, wasu na ganin cewa sai dai taimakon Allah kaɗai ne zai iya tabbatar da dorewar tasirin siyasar Barau, idan har rikicin cikin gida ya ci gaba da tsananta a cikin jam’iyyar.
KBC Hausa
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t