Abba Gida Gida abokina ne duk da kira da ya yi akan a cire ni — CP Bakori

IMG 20251013 WA0507

Daga Aminu Bala Madobi

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa duk da kiran da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya sauke shi daga mukaminsa, har yanzu yana da kyakkyawar alaka da gwamnan, tare da haɗin kai wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a jihar.

Bakori ya bayyana haka yayin taron manema labarai a Hedikwatar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano, inda ya ce “duk mu muna yin aikace-aikacenmu ne bisa doka, kuma har yanzu mu abokai ne, muna aiki tare don kare rayuka da dukiyoyi.”

A yayin taron, CP Bakori ya sanar da kama mutane tara da ake zargi da fashi da makami a sassa daban-daban na Kano. Ya ce cikin daya daga cikin hare-haren, barayin sun yi wa wata mata rauni har suka fitar mata da haƙori.

An kama su ne bayan wani hari da suka kai a Dorayi Babba, inda suka kwace mota, kuɗi har Naira miliyan 3.7, wayoyi, da wasu kayayyaki. Daga bisani jami’an ‘yan sanda suka gudanar da bincike wanda ya kai ga cafke sauran wadanda ake zargi a Kano da Kaduna.

Bakori ya ce an samo makamai, bindigogi, adda, wukake, fitilun hannu da motar da suke amfani da ita wajen aikata laifuka. Ya kuma tabbatar da cewa za a gurfanar da su kotu bayan kammala bincike.

Kwamishinan ya danganta nasarorin rundunar da shirin “Operation Kukan Kura”, wanda ya rage satar waya, fashi, da fadan ‘yan daba a Kano.

Ya kuma yabawa jami’an da suka gudanar da aikin bisa jajircewa da kwazo, yana rokon su su ci gaba da wannan aiki na tabbatar da tsaron Kano.

Shin Yakuke ganin kalaman Bakori?

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *