Alfijr ta rawaito shararren mawaƙin Kannywood, Ado Isa Gwanja ya maida martani ga wani lauya a jihar Kano, Barista Badamasi Sulaiman Gandu, wanda ya yi barazanar maka Hukumar Hisbah ta jihar Kano a gaban kotu, matukar ta gaza dakatar da Gwanja, daga fitar da wata sabuwar waka da ya yi mai taken “Asosa”
Alfijr Labarai
A makon nan ne dai Gwanja ya saki somin-taɓin waƙar a kafafen sada zumunta, inda a ka gano shi yana bin wakar tare da sosa jikinsa cewa kaikayi ya kama shi.
Tuni dai ƴan mata su ka cafe waƙar, inda su ke ta sakin faya-fayen bidiyo na TikTok su na yin rawan waƙar, tare da sosa jikinsu, a wani yanayi na warwasawa
Gwanja ya maida martani lokacin da gidan Freedom radio ya ji ta bakinsa, ya ce shi waka ce ya sani a matsayin sana’arsa kamar yadda shima lauyan, lauyanci ya sani a matsayin sana’arsa.
Alfijr Labarai
A cewar gwanja, tun tale-tale ake yin waƙar “Asosa” amma ba a ce komai ba sai da ya yi tashi sannan za ta yi zafi.
Ya ƙara da cewa tunda ya taso a rayuwarsa babu wata gwamnati, ko ta jiha ko ta tarayya da ta bashi aikin yi, sai da ya samu sana’a da kansa sannan kuma za a nemi a hana shi.
“Ni waka ma sani a matsayin sana’a kamar yadda shima lauyan, lauyanci ya sani a matsayin sana’a.
“Tun kafin a haife mu a ke waƙar Asosa amma ba a ce komai sai da Ni ma buga tawa?
Alfijr Labarai
“Babu wata gwamnati da ta bani aikin yi. Ni ne da kai na na samar wa da kai na sana’a, kuma shikenan sai a nemi a hana ni?,” In ji shi.