Daga Aminu Bala Madobi
Jam’iyyar APC reshen jihar Osun ta ce ba ta danasanin ficewar Omoluabi, daga jam’iyyar.
Omoluabi Progressives kungiya kuma jigo na jam’iyyar APC a Osun masu biyayya ga tsohon gwamnan jihar Rauf Aregbesola.
Kungiyar ta sanar da sauya shekar ta ne a karshen mako a yayin wani taron masu ruwa da tsaki a garin Ilesa na jihar Osun.
Taron ya samu halartar Aregbesola da sauran ‘ya’yan jam’iyyar APC na mazabu 332 na Osun.
An kaddamar da kungiyar siyasa ne a watan Agusta 2023.
Aregbesola yayi gwamnan Osun daga 2010 zuwa 2018, da kuma ministan harkokin cikin gida daga 2019 zuwa 2023 – a matsayin dan jam’iyyar APC.
A cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar Abosede Oluwaseun ya fitar, ya ce mambobin kungiyar sun yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar APC ne saboda “wariya da ake nuna musu daga jam’iyyar, dakatarwa da korar shugabanni ba tare da sauraron shari’a ba, da kuma ci gaba da tozarta tsarin”.
Oluwaseun ya ce ‘yan kungiyar sun bayyana shirinsu na komawa wata jam’iyyar siyasa gabanin zaben gwamnan Osun a 2026.
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Osogbo, kakakin jam’iyyar APC na jihar Osun, Kola Olabisi, ya ce ficewarsu ba zata tsinana komi ba a tafiyar jam’iyyar kasancewar sun yanke alaka da jam’iyyar tun shekarar 2022.
Kakakin jam’iyyar APC ya kuma yi gargadin cewa ficewar kungiyar shi ne mafarin “jana’izarsu ta siyasa,” inda ya kara da cewa ficewarsu za ta kai su ga rashin nasara a zaben gwamnan Osun na 2026.
“Sanarwar da kuka yi kwanan nan na ko dai kun kafa ko shiga wata jam’iyya ita ce mafarin jana’izar ku na siyasa, wanda zai kai ga jana’izar ku ta ƙarshe ta zaben gwamna na 2026. Abu mafi mahimmanci, mabiyan kungiyar ta Omoluabi Progressives da suka rufe ido za su yi nadamar kasancewa cikin wannan inuwa,” Acewar Olabisi.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp 👇👇
https://chat.whatsapp.com/FNMJaJ3I8Sc0bkkm8aJQbQ