Daga Aminu Bala Madobi
A ranar Laraba ne wa’adin ficewar kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso daga kungiyar ECOWAS, zai fara aiki bayan shafe shekara guda ana takun sakar siyasa, lamarin da ya wargaza yankin tare da barin kungiyar cikin makoma mara tabbas.
A ranar 29 ga Janairu, 2024, kasashen uku da gwamnatocin sojoji suke jagoranta sun sanar da ECOWAS a hukumance bukatarsu na janyewar cikin gaggawa. Amma a jawaban da ƙungiyar Afirka ta Yamma sun buƙaci sanarwar shekara guda don yin nazari.
Hakan dai zai faru ne a ranar Laraba, a yayin dukkan kasashen ukun suka yi watsi da kiran da kungiyar ECOWAS ta yi na su tsawaita wa’adin da watanni shida domin a samu mafita.
Kasashen Burkina Faso da Mali da Nijar a yanzu sun hade a wata karkashin wata kungiya mai suna kawancen kasashen Sahel (AES).
Sojojin dake jagorancin Gwamnatin kasashen sun zargi ECOWAS da kakaba musu takunkumi “ba bisa ka’ida ba” bayan juyin mulkin da ya kai su karagar mulki.
Sun kuma yi imanin cewa kungiyar ta yammacin Afirka ba ta taimaka musu da isashen kayan yaki da ta’addancin jihadi ba. ECOWAS, a cewarsu, tana biyayya ne ga masu mulkin mallaka na Faransa.
Paris na zamowa babbar abokiyar hamayyar gamayya na wadannan gwamnatocin mulkin soja, wadanda a yanzu ke goyon bayan kawance da kasashe irin su Rasha, Turkiyya da Iran.
Rikicin dai ta samo asali ne sakamakon juyin mulkin da aka yi a Nijar a watan Yulin 2023. Kungiyar ECOWAS ta yi barazanar afkawa Nijar ta hanyar sojoji don maido da hambararren shugaban kasar tare da kakabawa Yamai takunkumin tattalin arziki mai tsanani, wanda a halin yanzu aka cire shi.
A ranar Laraba ne kasashen uku za su fara amfani da fasfo dinsu na bai daya, kuma sun ba da sanarwar kafa rundunar hadin gwiwa ta mazajen soji 5,000 domin yakar masu jihadi nan ba da jimawa ba.
Kibucewar mambobin kungiyar uku da suka kafa zai “kawo rauni ga ECOWAS na daidaita rikice-rikicen siyasa a yankin”
Yanzu haka dai ana takun saka tsakanin kungiyar AES da wasu kasashen ECOWAS. Nijar ta ki bude kan iyakarta da kasar Benin, wadda ta zarga da karbar sansanoni inda masu jihadi ke atisaye, yayin da ta zargi makwabciyarta ta Najeriya da kokarin tada zaune tsaye.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp 👇👇
https://chat.whatsapp.com/FNMJaJ3I8Sc0bkkm8aJQbQ