Wata Sabuwa! ’Yan Bindiga Sun Kashe Wani Sabon Ango Sun Sace Amarya Da Iyalan Wani Kwamishina

Alfijr

Alfijr ta rawaito wasu ‘yan bindiga sun kashe wani sabon ango tare da sace matarsa mai ciki a garin Jere da ke karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna.

Maharan sun kuma yi garkuwa da wasu mutum hudu na iyalan tsohon kwamishinan yaki da fatara da talauci a jihar Kaduna, Abdulrahman Ibrahim Jere.

Wasu ganau sun ce ‘yan bindigar sun shigo garin Jere akan babura su sama da 50, sun kuma yi awon gaba da matar Angon da suka kashe, da wata jaririya da kanwar sa da kuma kanwar matarsa.

Alfijr

Mun yi kokarin jin karin bayani daga kakakin ’yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, amma hakanmu bai cimma ruwa ba

Slide Up
x