An Baiwa Wadanda Yan Sandan SARS Suka Ci Zarafi Da Azabtarwa Diyya

Alfijr ta rawaito hukumar kare hakkin dan adam a Najeriya, ta biya kusan dala dubu 700 diyya ga mutanen da ‘yan sanda suka azabtar da kuma ci zarafinsu a zamani SARS

Alfijr Labarai

Wasu da ga cikin mutane 58 da aka biya diyyar iyalai ko ‘yan uwan wadanda aka zabtar ne ko kuma sune da kansu.

Hakan ya biyo bayan bincike a kan korafe-korafen da iyalan wadanda aka azabtar suka yi in da suke zargin jami’an ‘yan sanda da kisan da shari’a ba ta amince da shi ba da batar da mutane ba dalili, da kame ba bisa ka’ida ba da tsare mutane na lokaci mai tsawo da kuma kwace musu kadarorinsu, musamman wanda rundunar ‘yan sandan nan da ta yi kaurin suna wato SARS ta yi.

Shugaban hukumar ya ce diyyar da aka biya hanya ce ta neman afuwa ga wadanda aka azabtar kuma gwamnati ta amince an take musu hakkokinsu.

Alfijr Labarai

Ya ce kada mutane su dauka cewa kudin diyyar da aka biya za su maye gurbin azabtarwa ko kuma laifukan da aka aikata na cin zarafin mutanen, ya kara da cewa hakkin hukumar ne ta kare ‘yancin al’ummar Najeriya.

A watan Oktobar 2020 ne, irin azabtarwa da cin zarafi da kuma take hakkin dan adam din da rundunar ‘yan sandan ta SARS ke yi ne suka haifar da mummunar zanga-zangar gama gari a duka fadin kasar.

BBC HAUSA

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *