Sojojin Sun Kashe Tarin ‘Yan Bindiga, Sun kubutar Da Wasu Da Aka Yi Garkuwa Da, Su 10

Alfijr ta rawaito Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga da dama tare da kubutar da mutane 10 da aka yi garkuwa da su a kananan hukumomin Chikun da Igabi na jihar Kaduna.

Alfijr Labarai

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Samuel Aruwan, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya ce sojojin sun kashe ‘yan bindigar ne a yayin da suke gudanar da aikin share fage a kananan hukumomin biyu, ya kuma kara da cewa an samu nasarar kwato wasu makamai.

Aruwan ya ce sojojin bayan fatattakar ‘yan bindigar sun kai farmaki maboyar tare da kubutar da wasu mutane 10 da aka yi garkuwa da su da aka daure su da sarka wasu kuma da igiya.

Aruwan ya bayyana wadanda aka yi garkuwa da su a sarka, Surajo Aliyu, Ayuba Yakubu, Ibrahim Abdulrasheed, Aliyu Mohammed, Magaji Tasiu, Nasiru Ahmed, Mohammadu lbrahim, Ayuba Abdulsalam, Kelvin Musa da Paul Patrick.

Alfijr Labarai

Kwamishinan ya ce, “Dakarun ‘Operation Forest Sanity’ sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga da dama tare da tarwatsa sansanonin a yayin gudanar da aikin share fage a wasu wuraren da ke da wuyar isa ga kananan hukumomin Chikun da Igabi.

Kamar yadda aka bayyana a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, sojojin sun yi nasarar kashe wasu ‘yan bindiga da ba a tantance adadinsu ba a yayin da suke fatattakar ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a Apewohe a karamar hukumar Chikun.

An kai farmakin har zuwa tsaunin Dakwala da Kunai da ke karamar hukumar, inda aka kara tarwatsa maboyar, duk da cewa ba a yi wata hulda da ‘yan fashin ba.

Alfijr Labarai

“Hakazalika an tarwatsa wani sansanin a wani wuri da aka fi sani da ‘Daban Lawal Kwalba’ a karamar hukumar Igabi, bayan da sojojin suka fatattaki ‘yan fashi da makami da ke gadin wadanda aka yi garkuwa da su.

Sojojin bayan sun fatattaki ‘yan bindigar sun kai farmaki maboyar tare da kubutar da mutane 10 da aka yi garkuwa da su, wadanda aka daure da sarka da igiya.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *