An Gudanar Da Gagarumar Zanga-zangar Lumana A Maiduguri

Alfijr

Alfijr ta rawaito al’ummar Maiduguri sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da karuwar ayyukan miyagun laifuka

Wasu mazauna gidan Shagari Low-cost da ke Maiduguri a ranar Asabar 12/02 /2022 sun gudanar da zanga-zangar lumana don nuna adawa da abin da suka bayyana a matsayin ‘yawan ayyukan aikata laifuka.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa zanga-zangar ta biyo bayan kashe wani Mista Aga Citi, mataimakin shugaban kungiyar masu sayar da katako a jihar.

Alfijr

An yi zargin wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba ne suka kashe mutumin a gidansa a ranar 10 ga Maris, da dare.

Masu zanga-zangar sun bukaci a rufe “Kasuwan Fara”, wani hadin gwiwar kasuwanci da aka sani da masu safarar miyagun kwayoyi, ‘yan kasuwa masu yin almundahana da sauran munanan ayyuka.

Daya daga cikin masu zanga-zangar Mista Felix Samuel, ya koka da yadda yawan aikata laifukan ya janyo fargaba a tsakanin mazauna yankin.

Alfijr

Samuel ya ce an kashe Citi ne a lokacin da ya ajiye motarsa, domin siyan kayan abinci mai. Ya kara da cewa idan ka zo Shagari Low-cost da yamma, za ka ga karuwai da matasa da dama daga sassa daban-daban na Maiduguri suna aikata duk wani abu na rashin da a da masha a, yanzu ba labari ba ne cewa ana kai wa mutane hari a kullum,” inji shi.

Malam Kabiru Musa, wani mazaunin yankin, wanda ya nuna damuwarsa kan yadda ake samun karuwar aikata laifuka a yankin, ya yi kira da a dauki matakan gaggawa domin shawo kan matsalar.

Muna kira ga Gwamna Babagana Zulum da ya kawo mana agaji domin ba za mu iya kwana da idanunmu biyu a rufe ba,” in ji Mal kabiru Musa.

Alfijr

Gaskiyar magana ita ce rana rana ana kai mana hari, ana kashe mu, ana fashin gidajen mu.

Malam Idris Wada, daya daga cikin masu zanga-zangar, ya ce gwamnatin Borno ta haramta duk wasu gidajen karuwai da sauran wuraren da ake yin karuwanci, fasikanci, sayarwa da shan miyagun kwayoyi tun daga shekarar 2017, amma wadannan ayyukan sun ci gaba da aikatawa.

Wada ya ce yayin da aka rufe gidajen karuwai da suka yi kaurin suna a Galadima, Artillery, Gamboru, Wulari, Hot Bite, Baga Road, Mairi da London Ciki, yawancin ayyukan sun taso ne a Shagari Low-cost.

Alfijr

Tsakanin shekarar da ta gabata zuwa bana, mazauna wannan yanki sun gano jarirai bakwai da wasu da ba a san ko su wanene ba suka jefar da su,” in ji shi.

Malam Mustapha Isa, daya daga cikin masu zanga-zangar, ya nuna fargabar cewa ayyukan ta’addanci da ake ta tafkawa zai haifar da mummunar illa ga jama’a, idan har aka ci gaba da yin hakan.

Alfijr

Ya kuma yi kira ga gwamnatin Borno da ‘yan sanda da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa da su kara zage damtse wajen yakar masu aikata laifuka da shaye-shayen miyagun kwayoyi domin kare al’umma da kuma kare lafiyar al’umma.

kwamishinan ‘yan sandan jihar Abdu Umar, ya umarci mutanensa da wasu ‘yan sintiri zuwa yankin domin gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa Citi.

Alfijr

Ya kuma yi kira da a kwantar da hankula, domin ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike na gaskiya domin gano bakin zaren tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin.

Shugaban ‘yan sandan ya kuma yi alkawarin zakulo masu aikata laifuka da masu tayar da zaune tsaye a jihar, ya tabbatarwa da mazauna garin cewa zai isar da sakon su ga gwamnan domin daukar matakin gaggawa kan matsalolin da suka taso.

Alfijr

A karshe kwamishinan ya jaddada kudurin rundunar ‘yan sanda na kare rayuka da dukiyoyi, inda ya bukaci jama’a da su kai rahoto ga jami’an tsaro mafi kusa da su domin daukar matakin gaggawa.

Slide Up
x