Shugaban Yan jaridun (internet) Na Kano, Yayi Kira Ga ‘Yan kungiyar, Kada Su Bari Ayi Amfani Dasu Wajan Yada Labaran Karya

Alfijr

Alfijr ta rawaito Shugaban yan jarida masu wallafa labarai a yanar gizo, (internet) reshen jahar Kano, Hisham Habib, yayi kira ga ‘ya’yan kungiyar da kada su bari ayi amfani dasu wajan yada labaran karya marasa tushe ko yada jitajita duba da karatowar zaben shekara mai zuwa (2023).

Shugaban yayi Kiran ne lokacin taron ganawa da juna na musamman da kungiyar ta gabatar ranar Asabar a Kano.

Acikin Jawabin sa da ke dauke da sa hannun Sakataren kungiyar, Yakubu Salisu, Hisham yace Kiran ya zama dole duba da tasirin kafafen yada labaran internet acikin al’umma yadda kowa ke amfani da wayar sa wajan bibiyar me ke faruwa a duniya.

Alfijr

Ya kuma Kara Kira da babbar murya ga ‘ya’yan kungiyar da su kasance kwararru akan aikinsu ako da yaushe, sanan ya kuma kara kira ga al’umma da ma’aikatu da su tantance kafafen yadda labaran da zasu yi mu’amula da su.

Sa hannu
Yakubu Salisu
Sakatare
12/03/2022