An Rufe Shahararren Kantin Jabi Lake Mall Da Ke Abuja Bayan Da Amurka Ta Sanar Da Harin Ta’addanci

Alfijr ta rawaito Katafaren Kantin nan dake birnin Tarayya Abuja Jabi, Lake Shopping Mall sun rufe bayan sanarwar ta’addancin da ofishin jakadancin Amurka suka sanar da za a iya yi a ƙasar.

Alfijr Labarai

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da tashe-tashen hankula na yiwuwar kai harin ta’addanci a babban birnin tarayyar Najeriya.

Akalla ma’aikatun kasashen waje guda biyar ne suka fitar da sanarwar gargadi ga ‘yan kasar da su guji tafiye-tafiye marasa mahimmanci zuwa babban birnin Najeriya saboda yiwuwar kai hari.

A cikin wata sanarwa da mahukuntan Shagon suka fitar, sun nemi afuwar abokan huldar su kan duk wata matsala da suka samu.

“Ga dukkan masu siyayyar mu masu daraja, Jabi Lake Mall za a rufe a yau, Alhamis, 27 ga Oktoba 2022.

Alfijr Labarai

An dauki wannan matakin ne domin kare lafiyar dukkan ma’aikata da abokan huldar kantin.

“Cibiyar Gudanarwa ta himmatu wajen rage duk wani cikas; duk da haka, amincin ma’aikatanmu da masu siyayya ya kasance mafi fifikonmu. In Ji sanarwar.

Hukumar gudanarwa na ci gaba da nazarin yanayin tsaro tare da tuntubar hukumomin tsaro da abin ya shafa kuma za su sanar da ku lokacin da za a sake bude kasuwar.

“Muna neman afuwar duk wata matsala da aka samu kuma muna fatan za mu samar muku da ingantacciyar hanyar siyayya nan ba da jimawa ba. Na gode.”

Alfijr Labarai

Jami’an tsaro sun kara sanya ido a babban birnin tarayya Abuja da kewaye domin dakile hare-haren.

An kuma kama wadanda ake zargin a wani samame da aka yi na hana zubar da jini a babban birnin Najeriya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *