APC Tayi Sabon Angon Shugaban Jam’iyyar Na Kasa

Alfijr ta rawaito Abdullahi Adamu Ya Zama Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa

Sanata Abdullahi Adamu Ya Zama Shugaban Jam’iyyar APC Na Kasa, Kimanin Shekara Daya Da Wata Tara Bayan Rushe Kwamitin Aiki Na Kasa (NWC) Adams Oshiomhole.

An zabi Abdullahi Adamu ne babu hamayya a ranar Asabar a babban taron jam’iyyar da aka gudanar a dandalin Eagle Square da ke Abuja, babban birnin kasar.

Alfijr

Gwamna Abubakar Badaru na jihar Jigawa ya sanar da Adamu a matsayin wanda ya lashe zaben bayan da ‘yan jam’iyyar da shugabannin jam’iyyar suka amince da shi ta hanyar kuri’a.

Ya shiga zaben ne a matsayin dan takarar da aka amince da shi bayan janyewar abokan takararsa daga takarar.

Slide Up
x