Yanzu Yanzu Engr Abba Kabir Yusuf Ya Fice Daga Jam’iyyar P D P

Alfijr ta rawaito Engr. Abba K Yusuf ya fice daga jam’iyar PDP ya koma jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) Mai kayan marmari, a hukunce.

Engr. Abba Yusuf Abba Gida-gida wanda ya kasance Dan Takarar Gwamna na PDP a zaben 2019, ya sauya sheka daga PDP zuwa NNPP a yau Lahadi a ofishinsa dake unguwar Diso dake karamar hukumar Gwale ta jihar Kano.