Asibitin Murtala Ya Samu Matsalolin Barin Ciki 13,291 A Shekarar 2021

Alfijr

Asibitin kwararru na Murtala Muhammad Kwararru a Kano ya samu matsalolin bari kimanin 13, 291 a cikin kaso 15,716 da suka je haihuwa a shekarar 2021 da ta gabata.

Alfijr

Jaridar KANO FOCUS ta ruwaito cewa babban daraktan hukumar kula da asibitocin jihar Nasir Alhassan Kabo ne ya bayyana haka a ranar Laraba yayin da yake raba kayayyakin masarufi kyauta ga manyan asibitoci da cibiyoyin lafiya a matakin farko a jihar Kano.

Kabo, wanda daraktan kula da lafiya Sulaiman Mudi Hamza ya wakilta ya bayyana cewa asibitin ya karbi marasa lafiya 18, 848 yayin da 1,466 suka samu nasara daga aikin tiyata tare da kayayyakin kiwon lafiya kyauta da ake rabawa kowane asibitoci sama da dari da ashirin a fadin jihar.

Da yake gabatar da magungunan sama da N13m, Darakta janar ya ce magungunan da aka bayar sun hada da na hatsari na bangaren gaggawa, na haihuwa da kuma kula da yara.

Ya mika godiyarsa ga kwamitin da aka yi wa rabon tare da sanya ido kan sadaukarwarsu da kuma asusun kula da lafiya na jihar Kano da suka bada tallafin N5.5m a wannan watan.

Slide Up
x