Innalillahi wa inna ilaihirraji un! ‘Yan Ta’adda Sun Kashe DPO a Wani Sabon Hari a Katsina

Alfijr

Alfijr ta rawaito wasu ‘yan ta’adda sun kashe jami’in ‘yan sanda mai mikamin DPO a wani hari da suka kai garin Jibia da ke karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.

Alfijr

Jami’in tsaron da aka kashe, A. A. Rano, har zuwa rasuwarsa shi ne jami’in da ke kula da shalkwatar ‘yan sanda da ke Jibia, kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana a ranar Laraba.

Ko da yake ba a iya tantance hasarar da ‘yan bindigar suka yi ba, mazauna yankin sun ce an kashe soja guda tare da jikkata wani.

Alfijr

Wata majiya da ta tattauna da Alfijr ta ce, wannan abin duka yana faruwa ne a Jiba saboda hakar zinare da ake a garin,

Sati biyu da suka wuce, shi wannan DPO da aka kashe yau da Asuba, ya bada sanarwa a masallatan juma’a na Jibia cewa mutane su dena hakar zinare, saboda a kansa ne ake yawan hari a garin, amma mutane sunki su dena, gashi an hallakashi yau

Alfijr

Allah ya jikansa da rahama Allah ya kawo mana karshen wannan masifun, Allah ya tsare mana Jami an tsaronmu da sauran al umma baki daya ameen.

Slide Up
x