ASUU Ta Kara Tsawaita Yajin Aikinta Da Sati Takwas (8)

Alfijr

Alfijr ta rawaito kungiyar ASUU, ta sanar da tsawaita wa’adin yajin aikin da suka tafi zuwa makwanni 8 sakamakon rashin cimma matsaya da gwamnati kan bukatunsu.

ASUU ta shiga yajin aikin ne sakamakon gazawar gwamnatin Muhammadu Buhari wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’a na kasar.

Farfesa Abdulkadir Muhammad Danbazau jami’i ne a kungiyar ta ASUU, ya ce sun dauki matakin kara wa’adin ne domin bai wa gwamnati damar cimma sahihiyar matsaya, ta yadda ba sai sun kara tafiya wani yajin aikin nan gaba ba.

Alfijr

Ya ce makwanni 8 sun wadatar matukar gwamnatin da gaske take kan daukar matakin da ya dace, domin suna ganin wannan itace hanyar karshe da za su bi, don biyan bukatunsu.

Tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabarairu ne kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamanatin Najeriya na tsawon wata guda.

Slide Up
x