Da Dumi Duminsa! Kotua Ta Soke Belin Dan Sarauniya Ta Ba Da Umarnin A Kama Shi

Alfijr

Yanzu-yanzu: Kotu ta soke belin Ganduje, ta kuma ba da umarnin a kama shi

Kotun Majistare ta Jihar Kano mai lamba 58 karkashin jagorancin Aminu Gabari ta soke belin da ta bayar tun da farko ga mai sukar Ganduje a shafukan sada zumunta, Mu’a’zu Magaji Dansarauniya kan rashin halartar kotun har sau 3 domin amsa tuhumar da ake masa.

Hakazalika kotun ta bayar da umarnin a kama shi da laifin bata sunan gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, tare da kira ga masu tsaya masa guda biyu da su bayyana ranar 28 ga watan Maris.