Alfijr ta rawaito ana sa ran babban bankin Najeriya zai lalata kudaden da suka lalace da kuma tsofaffin kudaden da suka haura N6tn idan wa’adin mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kare a watan Mayun 2023, a wani bincike da jaridar PUNCH da jaridar Nigerian Tracker suka yi ya nuna.
Alfijr Labarai
Tuni dai bayanai da aka samu daga rahoton shekara-shekara na sashen gudanar da hada-hadar kudi na babban bankin Najeriya CBN tsakanin shekarar 2016 zuwa 2020 ya nuna cewa babban bankin ya lalata tarkacen takardun kudin da ya kai N4.1tn a tsawon shekaru biyar.
Wakilinmu ya kasa samun cikakkun bayanai kan adadin kudaden da babban bankin Kasar da ya lalata a shekarar 2021 da 2022 har zuwa lokacin da ake hada bayanai a ranar Lahadi.
Sai dai ana sa ran babban bankin zai lalata sama da kashi 80 cikin 100 na takardun kudi na N3.23tn da ke yawo a halin yanzu sakamakon matakin da ya dauka na sake fasalin N100, N200, N500, da N1,000.
Alfijr Labarai
Matakin dai zai kawo jimillar kudaden Naira da gwamnati mai ci ta lalata zuwa akalla N6tn.
Gwamnan babban bankin kasar CBN, Godwin Emefiele, ya sanar a ranar Larabar da ta gabata cewa bankin zai sake fitar da wasu takardun kudi na naira a ranar 15 ga watan Disamba, 2022.
Emefiele ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai na musamman a Abuja inda ya bayyana dalilan daukar matakin.
Alfijr Labarai
A cewar gwamnan babban bankin na CBN, an dauki wannan mataki ne da nufin shawo kan tabarbarewar kudaden waje da kuma dakile kudaden jabu da biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane da ‘yan ta’adda.
A halin da ake ciki kuma, takaitattun bayanan bankin na CBN na shekarar 2016-2020 ya nuna cewa a shekarar 2016, babban bankin ya lalata zunzurutun kudi har N829.94bn.
A shekarar 2017, CBN ta sake lalata zunzurutun kudi N977.23bn na kudaden banki da suka lalace.
Alfijr Labarai
Shekarar 2018, 2019 da 2020 an lalata N814.59bn, N814.44bn da N698.59bn, bi da bi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb