Jirgin Birtaniya Ya Dawo Da Sauka Da Tashi A Abuja Babban Birnin Najeriya

Alfijr ta rawaito Jirgin saman Birtaniya da ya dakatar da jigilar a Nijeriya sakamakon wata rashin fahimta ya dawo kan aikinsa daga Abuja zuwa Landan.

Alfijr Labarai

Jirgin mai lamba BA83 ya soke zuwansa Abuja a ranakun Juma’a da Asabar, awanni 24 bayan ya karkata saukarsa zuwa jihar Lagos.

Wannan mataki ya fusata fasinjoji masu tafiya kasashen waje, inda suka rika kokawa da cewa kamfanin jirgin bai sanar da su daukar wannan matakin ba, sai kawai jin dakatarwar suka yi.

Wata majiya ta ce, karkatar da jirgin zuwa jihar Lagos ba zai rasa nasaba da sanarwar da ofishin jakadancin Amurka ya fitar ba na yiwuwar kai harin ta’addanci ba.

Alfijr Labarai

Kwanaki biyu bayan kurar gargadin ta lafa ne sai ga shi kamfamin ya dawo da sauka da tashi daga Abuja daga ranar Lahadi 30 ga watan Oktoba.

Sanarwar ta ce jirgin zai rika tashi daga Abuja ne da karfe 8:00 ya kuma sauka a filin jirgin sama na Heathrow da ke kasar Burtaniya da karfe 6:25 na yamma.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *