Alfijir Labarai ta rawaito Sanatocin Nijeriya sun zabi Barau Jibril a matsayin sabon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan kasar.
An zabi Sanata Godswill Akpabio a matsayin shugaban majalisar dattawa ta 10 bayan wani zaman da aka yi a zauren majalisar.
Akpabio, wanda tsohon gwamnan jihar Akwa-Ibom ne kuma dan majalisa daga Akwa Ibom ta Arewa-maso-Yamma ne ya lashe zaben bayan ya samu kuri’u 63.
Shi ne wanda aka tsayar dan takarar jam’iyyar shugabancin majalisar na APC, amma sai Sanata Abdulaziz Yari daga Zamfara ta Arewa maso Yamma ya kalubalance shi, wanda shi ma dan jam’iyyar APC ne.
Tun da fari Sanata Ali Ndume ne daga Borno ta Kudu ya zabi Akpabio, yayin da zababben Sanata Elisha Abbo daga Adamawa ta Arewa ya zabi Yari.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijir Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ