Bayan Da Ake Zargin Ɗan Sanda Da Yiwa Ƴar shekara 17 fyaɗe, Kwamishina Ya Bada Umarnin Bincike
 

Alfijr ta rawaito Kwamishinan ƴan Sandan jihar Enugu, Ahmad Ammani, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan wani mataimakin Sufetan ‘yan sanda, ASP, kan zargin yi wa wata ƴar shekara 17 da ke tsare fyaɗe.

Alfijr Labarai

Umurnin binciken na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Daniel Ndukwe ya fitar a Enugu a ranar Asabar.

Kwamishinan ya umarci sashen binciken sirri da manyan laifuka na rundunar da ya gudanar da cikakken bincike tare da gabatar da cikakken sakamakon kan wannan zargi.

Ya bayyana cewa duk da cewa lamarin da ake zargin ya faru ne a ranar 18 ga Maris, 2022, iyayen wacce ake tsare da ita ɗin sai kwanan nan su ka kawo rahoton.

Alfijr Labarai

Jami in mai Mukamin ASP yana aiki ne a caji ofis, na Awgu da ke jihar Enugu.

Kwamishinan ya kuma ba da umarnin a kammala binciken cikin ƙanƙanin lokaci.

Ya kuna ba da tabbacin cewa za a yi abinda ya dace, matukar aka sami ko wanene da laifi to za a hukunta shi yadda ya kamata,” in ji Sanarwar

Slide Up
x