Wanene Marigayi Mal Habibu Babura? Yau Shekara Hudu Da Rasuwarsa


Marigayi Dr Habibu Sani Babura, an haife shi a ranar 4 ga watan Janairu 1952, A Garin Babura Dake tsohuwar Jihar Kano, wanda yanzu haka take a jahar Jigawa.

Alfijr Labarai

Marigayi Mal Habibu ya kammala karatunsa na sakandare ya rubuta jarrabawarsa ta kammalawa a shekarar 1972 wato “WAEC”

Daga nan ne marigayin ya tafi Jami’ar Amadu Bello da ke Zaria yayi karatunsa na Share Fagen shiga jami’ar tsawon watanni 18.

Ya fara karatun Digirinsa na farko a bangaren Hausa, kuma ya kammala a shekarar 1977.

Alfijr Labarai

Dr Babura yana daya daga cikin rukunin dalibai na 4 da suka fara karantar harshen  Hausa a duk Fadin ƙasar Nigeria.

Bayan da marigayin ya kammala karatun digiri a ABU Zaria,ya tafi bautar kasa wato (NYSC) a jihar Borno a shekarar (1977-1978).

Alfijr Labarai

Mal Habibu ya fara aikin koyarwa a Jami’ar Bayero da ke Kano, sai da ya shafe shekaru 38 yana koyarwa a Jami’ar tare da hidimtawa al umma.

Marigayin ya hadu sa hatsarin mota a shekarar 1982 a kan titin Kabuga, akan hanyarsa ta zuwa wurin aikinsa jami’ar Bayero Dake Kano.

Hakan yayi sanadiyar samun karurar mutuwar barin jiki, wanda hakan tasa dole sai dai, ana turashi a kujera (Wheelchair).

Marigayin ya taka muhimmiyar rawa ga al umma, kama daukar nauyin karatun yara da manya daga Kano,  Jigawa, Kasar Nijar da sauran al ummar Kasar nan.

Marigayin ya zaune ne da iyalansa mata biyu a cikin jami ar daga bisani ya dawo unguwar Janbulo, bayan samun lalurar tasa sai ya sawwakewa matan nasa don karya tauyesu! Allahu akbar na Allah mutumin Allah.

Alfijr Labarai

Gidan marigayin sai da ya koma gidan dalibai, saboda duk wasu dalibai da suka zo daga Babura ko kuma Jamhuriyar Nijar, kuma suka rasa wurin kwana a Jami’ar Bayero, to sai su koma gidan Mal Habibu da zama ko ya sani ko bai sani ba.

Babban abun mamaki ga rayuwar marigayin shine, lalurar da ta sameshi, hakan bai hana shi aikinsa da kuma uwa uba hidimtawa al’umma ba, asali ma kamar kara masa kaimi aka yi wajen cigaban al umma, hatta ni da nake magana Musa Best seller Mal Habibu shine sanadin dorewar karatuna da cigaban rayuwata wallahi.

Alfijr Labarai

Kafin komawarsa ga mahaliccinsa, Mal Habibu ya yi wani shiri mai farin jini hadi da Ilimantar wa, wato Aiki Da Hankali a fitaccen gidan rediyon nan mai zaman kansa wato freedom Radio.

Shirin nan fa ya zama wata sabuwar Jami ar Hausawa wanda ba sai kaje aji ba zaka koyi ilmi.

Mal Habibu Babura ya koma ga Allah ne a ranar 4/09/2018, wanda wannan rana ita ce shekera 4 rabon mu da. Masoyin Annabi

Alfijr Labarai

Allah ya shafe kura kuransa, Allah ya sada shi da masoyinsa Annabi Muhammadu S A W

Slide Up
x