Daga A’isha Salisu Ishaq
Ayyukan sauka da tashin jiragen sama sun dawo daidai, bayan tsaikon da aka samu na wasu sa’o’i sakamakon faduwar da jirgin saman kamfanin Max Air ya yi a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke jihar Kano.
A daren Talata ne jirgin ya tunkuyi ƙasa yayin sauka a filin, inda tayoyin sa su ka kone garin saukar.
Sai dai ba a samu asarar rayuka ko jikkata a haɗarin ba.
Da ya ke bayani ga wakilin Daily Nigerian Hausa, wani babban jami’i a filin jirgin saman na Kano, wanda yx nemi a sakaya sunan sa, ya ce al’amura sun daidaita kuma tuni ma aka janye jirgin daga kan titin jirgi.
Ya ce tun misalin ƙarfe 4 na asuba aka janye jirgin.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ