An gwabza fada a hedikwatar jam’iyyar PDP, inda ake gudanar da taron kwamitin amintattu na jam’iyyar (BoT).
Rikicin dai ya fara ne lokacin da aka hana Sunday Ude-Okoye, wani jigo a jam’iyyar damar halartar taron.
Jam’iyyar PDP dai ta shiga wani sabon rikicin shugabanci a daidai lokacin da Samuel Anyanwu da Ude-Okoye ke ikirarin zama sakataren jam’iyyar na kasa.
A watan Disamba 2024, kotun daukaka kara ta yanke hukuncin cewa Ude-Okoye ya maye gurbin Anyanwu a matsayin sakataren PDP na kasa.
Kwamitin zartarwa na shiyyar kudu maso gabas na jam’iyyar ta tsayar da Udeh-Okoye a matsayin wanda zai maye gurbin Anyanwu bayan ya zama dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Imo a 2023.
Anyanwu ya samu wasu umarnin kotu na hana tsige shi daga mukaminsa.
Sai dai a wani hukunci da ya yanke a ranar 20 ga watan Disamba, 2024, Ridwan Abdullahi, alkalin kotun daukaka kara, ya yi watsi da hukuncin da babbar kotun ta yanke, wanda ya hana a tsige Anyanwu, saboda “rashin cancanta”.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ