Gwamnan Jihar Kano, ya bayyana cewa ana kan hanyar yanke shawarar cire wasu mambobin majalisar zartarwa da aka tantance kwazonsu a ƙarƙashin abin da aka tsara su yi.
Alfijir labarai ta rawaito Gwamnan, wanda ya tabbatar da karɓar rahoton kwamitin duba aikin mambobin majalisar, ya bayyana cewa, jama’a za su ji matakin da gwamnati za ta ɗauka nan ba da jimawa ba, kamar yadda mai magana da yawunsa Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya baiyana a wata sanarwa.
Gwamnan ya tunatar da al’umma game da shirin sauya wasu daga cikin mambobin majalisar a wata hira kai-tsaye da aka yi da shi ta gidan rediyo tare da wasu kafofin yada labarai da aka gudanar a Fadar Gwamnati a ranar Laraba.
Ya bayyana cewa rahoton ba zai yi amfani ba yanzu, saboda kasancewarsa tare da su a tsawon shekara ɗaya da rabi ya ba shi damar sanin ƙwarewar su sosai, don haka zai yanke hukuncin karshe game da su da kansa.
Ya bayyana cewa babu ɗaya daga cikin kwamishinonin da suka riƙa neman mukamin, yana mai jaddada cewa kafin naɗin su, ya yi la’akari da ƙwarewa, amana, da kuma shawara daga masu bada shawara.
Ya ce abin da nake buƙata daga kwamishinoni shi ne su kasance masu biyayya gare ni, ga jam’iyyar NNPP, da kuma Tafiyar Kwankwasiyya, tare da jajircewa a kan aikin su da kuma kawo sabbin dabaru don cigaban jihar.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj