Labari Mai Dadi! Ɗan majalisar wakilai Engr sagir koki ya ɗauki nauyin aikin ido ga dubban al’umma a Kano

Alfijir labarai

Ɗan majalisar wakilai a tarayyar Najeriya Engr sagir koki ya dauki nauyin aikin ido da duba lafiyar sa ga dubban al’ummar karamar hukumar birnin Kano.

Alfijir labarai ta rawaito ayyukan da ɗan majalisar ya fara ya kunshi duba lafiyar idon don bada magani, wasu kuma duba su don basu gilashi, wasun su kuma zasu amfana da aikin idon kamar yadda ya gudanar.

Tsarin da aka yi wajen wannan aikin ya haɗar da, duk wata mazaba a karamar hukumar birnin Kano goma sha uku 13, ta amfana da mutane dari da wani abu daga cikinta.

Hakazalika Engr Sagir Koki duk mazaba ya debi yara an tura su makarantar school of Nursing suna karanta aikin lafiya. Ya kuma himmatu wajen ayyukan alheri a wannan yanki nasa.

An gudanar da wannan aiki ne tare da kwararrun lilitoci masana lafiyar ido a gidan sarki kofar kudu a ranar yau jama’a 8 Nov 2024

1000588669
Aikin ido

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *