Da Ɗumi Ɗuminsa! BBC Ta Karyata Cewar Zata Rufe Shashinta Na Hausa.

Alfijr ta rawaito bayan yadda wasu kafafen watsa labarai suka cika da wasu labarun cewar BBC zasu rufe shashinsu na Hausa bayan kafuwarsa sama da 60 ana yaɗa labarai.

Alfijr Labarai

Bayan karo da wannan labarin Alfijr bata yi kasa a guiwa ba, ta tuntubi jami’an BBC don fayyace gaskiyar lamarin.

Da farko dai ina mai tabbatar maka da cewar wannan labarin ba gaskiya bane labarine na kanzon kurege, kuma mara tushe. In Ji Majiyar.

Tabbas akwai sauye-sauye da aka shirya yi ba a Sashen Hausa na BBC kadai ba, har da wasu harsuna da BBC ke watsa labarai a kasashen Afirka da na Asia har da Turai.

Hakazalika zamu daina shirin talabijin ne kawai, amma radiyo dana shafukan sada zumunta suna Nan daram.

Alfijr Labarai

Majiyar ta kara da cewa yaya za ka yi zubin dashi shekaru 64, sai da dauka ya zo kanka kace ka daina baka so! Bature ai ba mahaukaci bane.

Nan da yan kwanaki za muyi bikin Gwarzon hikayata a nan Abuja tare da murnar cikarmu shekaru 65, da kafuwa. In Ji majiyar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *