Da Ɗumi Ɗuminsa! Gwamnatin Kano Ta Shirya Tsaf Don Daukan Sababbin Ma aikata

Alfijr Labarai

Alfijr ta rawaito Gwamnatin Jihar Kano karkashin Gwamna, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta shirya Tsaf kuma ta kafa kwamiti domin karbar takardun neman aiki ga masu bukatar aikin a fadin jihar.

Masu Sha awar wannan dama zasu shigar da bayanan bukatar su daga ranar Litinin 8/08/2022 zuwa Juma’a 12/08/2022 domin tantancewa

Alfijr Labarai

Sanarwar ta kuma cewar, duk mai bukata zai shiga ta wannan site din wanda za’a bude ranar litinin don cike bayanansa ko bayananta ta

www.kahucee.com.ng

Wadanda zasu iya cin gajiyar wannan neman aiki ya kadance a kalla suna da shaidar karatu na

DIPLOMA.

NCE.

HND.

Bsc.

Wannan sanarwar ta fito ne ta bakin Engr. Rabiu Suleiman Bichi a madadin gwamnatin jihar kano

Alfijr Labarai

Wanda ya ji wannan sanarwar ya sanar da yan uwa don samun amfana.