Alfijr ta rawaito Duk da cewa kungiyar ba ta fitar da sanarwar a hukumance ba amma, an dauki matakin ne a karshen taron majalisar zartarwa ta kasa ta kungiyar da aka gudanar a sakatariyar ASUU da ke Abuja.
Alfijr Labarai
Dakta Chris Piwuna, mataimakin shugaban kungiyar ta ASUU ya tabbatar da hakan, inda ya ce an janye yajin aikin ne da sanyin safiyar yau Juma’a, bayan da shugabannin kungiyar suka gana cikin dare a Abuja babban birnin tarayya.
Kotun kolin Najeriya ta umarci kungiyar ta janye yajin aikin gabanin ta saurari daukaka karar da ta yi a gabanta.
Biyo bayan yadda gwamnatin Tarayya Ta garzaya gabanta domin a taka kungiyar yan kwadagon birki kan matakin yajin da suka dauka tsawon lokaci.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller