Alfijr ta rawaito bayan sa’o’i 24 da yin garkuwa da mahaifiyar dan takarar Sanatan Kano ta tsakiya, AA Zaura, jami’an tsaro na farin kaya, DSS sun ceto ta a jihar Jigawa.
Idan kun tuna, wasu ‘yan bindiga da yawansu ya kai, sun kai hari garin Zaura da ke karamar hukumar Ungogo a jihar Kano sun yi garkuwa da mahaifiyar dan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya, A.A Zaura, a ranar Litinin din da ta gabata.
Shugaban karamar hukumar Ungogo, Engr. Abdullahi Garba Ramat ya tabbatarwa da Solacebase a ranar Talata cewa an ceto ta a jihar Jigawa.
Alfijr
Haka kuma, wani babban jami’in DSS wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da cewa jama an sun ceto Laure da wata tsohuwa da aka yi garkuwa da su kusan kwanaki goma.