Wani Magidanci Ya Maka Jaruma Hadiza Gaban A Gaban Kotun Shari’ar Musulunci

Alfijr

Alfijr ta rawaito wani maigidanci ya maka jarumar Kannywood, Hadiza Gabon, a gaban wata kotun shari’ar Musulunci da ke Kaduna saboda ta ki amincewa ta aure shi.

Maigidancin, mai suna Bala Musa, ya shaida wa kotun cewa sun jima suna soyayya da jarumar, bisa alkawarin za ta aure shi, amma ta ci gaba da yaudarar shi.

Bala ya ce, “Ya zuwa yanzu, na kashe mata kudi kimanin N396,000, ya kara da cewa duk lokacin da ta tambaye ni kudi na kan kashe mata ba tare da bata lokaci da da niyyar zamu yi aure.

Alfijr

Amma ko da na gayyace ta zuwa Gusau, babban birnin Jihar Zamfara inda nake da zama, don gaisawa da magabatana sai ta ki zuwa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa an fara sauraron karar ce tun a ranar 23 ga watan Mayun 2022, amma Hadizan ba ta halarci zaman kotun ba.

Alfijr

Lauyan jarumar, Mubarak Kabir, ya shaida wa kotun cewa wacce yake karewa ba ta halarci zaman ba ne tun a lokacin saboda rashin sanin sahihancin takardar sammacin da aka kai mata.

Mubarak ya kara da cewar, matsayin wacce nake karewa na Shahararriyar Jaruma, mutane da yawa kan je wajenta da manufofin daban daban, don haka dole sai tana taka-tsantsan.

Alfijr

Daga nan sai ya roki kotun da ta ba shi karin lokaci don ya gabatar da ita a gaban kotun.

A nan ne alkalin kotun, Mai Shari’a Rilwanu Kyaudai, ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 13 ga watan Yuni mai zuwa

Kamar yadda Aminiya ta wallafa

Slide Up
x