Da Ɗumi Ɗuminsa! Mutane Da Yawa Sun Mutu A Wani Hadarin Jirgin Sama

Alfijr ta rawaito Mutane da yawa sun mutu bayan da wani jirgin fasinja ya yi hatsari a tafkin Victoria a Tanzaniya yayin da yake kokarin sauka a filin jirgin sama.

A cewar rahoton da kafar yada labarai ta Tanzaniya TBC a safiyar Lahadi, 6 ga watan Nuwamba, 2022, jirgin fasinja ya taso daga Dar es Salaam ya nufi Bukoba ta Mwanza.

An ce musabbabin faduwar jirgin ya biyo bayan ruwan sama da iska mai karfi a lokacin da yake kokarin sauka a filin jirgin na Bukoba.

Hotunan bidiyo da hotuna da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna jirgin ya kusa nutsewa, sai dai jelarsa mai launin kore da launin ruwan kasa da ake iya gani a saman layin ruwa.

An tura kwale-kwale masu aikin ceto tare da ceto akalla mutane 15 da harin ya rutsa da su, yayin da wasu fasinjojin suka makale a cikin jirgin.

A halin da ake ciki, shugabar kasar Tanzaniya Samia Suluhu Hassan ta yi kira da a kwantar da hankula yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

“Na kamu da bakin ciki labarin hatsarin da ya shafi jirgin Precision Air,” ta wallafa a shafinta na twitter.

“Mu kwantar da hankalinmu a wannan lokaci da masu aikin ceto ke ci gaba da aikin ceto tare da addu’ar Allah ya taimake mu.” In ji Ta

Filin jirgin saman Bukoba yana kan gabar tafkin Victoria, tafkin mafi girma a Afirka.

Precision Air shine babban jirgin saman Tanzaniya mai zaman kansa.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *