Alfijr ta rawaito Gwamnatin Jihar Kano tayi martani game da wani rahoto da kafar yaɗa labarai ta Sahara Reporters ta wallafa, wadda ta bayyana cewa Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Yana daga cikin Gwamnonin da aka samu Maƙudan Ƙuɗaɗe a gidajensu.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano kwamarade Muhammad Garba shi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar aka kuma rabawa manema labarai
Muhammad Garba yace labarin bashi da tushe ballantana makama dan haka al’umma suyi watsi dashi.
Ya ƙara da cewa bayan sanarwa da hukumar EFCC ta fitar a kan wasu Gwamnoni 3 da tace tana sanya idanu akansu, bata bayyana sunan Gwamnonin ba.
To amma jaridar Sahara Reporters ta kama sunan Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda kuma hakan ya saba da ka’ida.
Muhammad Garba yace wajibine Jaridar ta Nemi yafiyar Ganduje bisa abinda ta wallafa wanda ba gaskiya bane.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux
Allah ya cigaba da haskaka mana ta hanyar yada labarai ku da muke jin dadin su
Saboda iya aikin ku majarida
Muna jin daɗin yadda kuke gudanar da ayyukan Ku bisa kwarewa da gabatar da sahihan labaru
Allah ya. Saka da alheri muna godiya da kulawarku