
Alfijr ta rawaito Babban hafsan sojin Nijeriya Lt Gen Faruq Yahaya ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya da cewa sojoji ba za su ba ‘yan kasa kunya ba wajen sauke nauyin da aka dora musu na kare martabar kasa da ‘yan kasa.
Ya bayyana hakan ne a garin Kwantagora a lokacin kaddamar da shirin yaki da ta’addanci mai lakabi ‘Operation Mugun Bugu’.
Daraktan watsa labaran hedikwatar tsaro ta kasa Brig Gen Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan in da ya ce wannan sabon shirin babu irinsa a inda ake horar da sojoji dabarun yaki daban-daban domin samar da tsaro ga ƙasar baki ɗaya.
Onyema ya tabbatar da cewar wannan horo zai taimaka sosai wajen samar da sabbin dabaru ga sojojin da kara musu azama wajen yaki da ta’addanci.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux