Wata Mummunar Gobara Ta Tashi A Kasuwar Badume Da Bichi Jihar Kano

Alfijr ta rawaito Hukumar kashe gobara jihar Kano ta tabbatar da tashin wata gobara a kasuwar sayar da Tumatur da ke Badume a ƙaramar hukumar Bichi.

Kakakin hukumar ta kashe gobara Saminu Abdullahi Yusuf ya bayyana haka yana mai cewa ofishin hukumar na Bichi ne ya samu kiran gaggawa da misalin karfe 3:30 na dare daga Ibrahim Tsalha wanda ya bada rahoton tashin gobara a kasuwar Badume ta karamar hukumar Bichi.

Ya ce, jami’an hukumar sun isa wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 03:35 sai suka gano cewa, wani fili mai fadin mita 200 da tsawon mita 200 da ake yin amfani da shi a matsayin kasuwar tumatur ta Badume ya kama da wuta.

Saminu ya bayyana kimanin shaguna na wucin gadi guda 100 ne a wurin da iftila’in ya faru yayin da mutum uku suka makale kuma har yanzu ba a tabbatar da sunayensu ba, mace daya mai kimanin shekara 35 gurgu daya mai kimanin shekaru 30 da haihuwa, sai kuma mutum na karshe mai kimanin shekaru 18.

Dukkanin wadanda harin ya rutsa da su, an ceto su ne ba a hayyacinsu ba, daga baya kuma aka tabbatar sun mutu, inda aka mika wadanda abin ya shafa ga Sufeto Mukaila Inusa jami’i a ofishin ‘yan sanda na Bichi.

Don haka tare da kokarin mutanenmu mun yi nasarar ceto shaguna na wucin gadi 100 a yankin.

Kakakin ya bayyana hukumar na nan na binciken musabbabin faruwar lamarin.

Ya ƙara da cewa, zan yi amfani da wannan kafofin yada labarai don jawo hankalin jama’a don kashe duk na’urorin lantarki da kuma cire haɗin daga tushen lokacin da ba a amfani da su da kuma kula da wuta.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *