Da Ɗumi Ɗuminsa! Yan Kasar Lebanon Sun Samar Da Katafaren Asibiti Na Zamani A jihar Kano

Alfijr ta rawaito Ƴan kasar Lebanon mazauna Kano sun samar da wani asibiti na zamani a babban jihar.

Alfijr Labarai

Kakakin yada labarai na masarautar Kano Balarabe Ƙofar Na isa ne ya bayyana hakan lokacin da Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kai ziyarar gani da ido a ranar Litinin a unguwar Bompai.

Ya bayyana asibitin na ɗauke da gadajen kwanciya 25, ga kuma na’urori na zamani domin gwaje-gwajen cututtuka daban daban, baya ga dakin haihuwa, da kuma kula da jarirai.

Mai Martaba Sarkin Kano ya nuna farin cikinsa da samar da asibitin, ya kuma ce hakan wani babban cigaba ne da ya zo wa al’ummaar jihar kano baki ɗaya.

Alfijr Labarai

Sannan ya ce, asibitin zai rage yawan fita waje da ƴan Najeriya ke yi domin neman lafiyarsu.

Shugaban asibitin, Abbas Hajaaj a nasa jawabin, ya ce sun samar da asibitin ne domin kishin jihar Kano da al ummarsa baki ɗaya.

Ya kuma bayyana cewa an sanya wa asibitin suna asibitin ƴan Nijeriya da ƴan Lebanon.

Ya Kara da cewar, nan ba da daɗewa ba za a yi bikin kaddamar da shi, bayan kammala ɗaukar sabbin likitoci da ma’aikatan jiyya da na gudanarwar asibitin.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *