Da Ɗumi Ɗuminsa! ‘Yan Ta’adda Sun Sake Sakin Wasu Fasinjojin Jirgin Kasa Bakwai Da Aka Sace

Alfijr Labarai

Alfijr ta rawaito wasu fasinjoji bakwai da aka yi garkuwa da su a harin jirgin kasa na ranar 28 ga Maris a jihar Kaduna sun samu ‘yanci.

Alfijr Labarai

An sako mutanen ne  a safiyar Laraba bayan sun shafe kwanaki 135 a hannun ‘yan ta’addan, sai dai ba a bayyana ko an biya kudin fansa ga ‘yan ta’addar domin a sako su ba.

Wani mamba a kungiyar Tukur Mamu a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba ya ce shida daga cikin wadanda aka sako ‘yan gida daya ne, wadanda suka hada da ma’aurata da ‘ya’yansu hudu.

Sanarwar ta ce an sako yaran da iyayensu ne bayan da Sheik Ahmad Gumi ya shiga tsakani.

Mahaifin yaran hudu, Abubakar, dan tsohon shugaban mulkin soja na jihohin Kano da Benue, Manjo Janar Idris Garba (RTD) ne, kuma
ma’aikaci ne na Hukumar Majalisar Dokoki ta Kasa.

Alfijr Labarai

‘Yan ta’addan sun kuma sako wata mata ‘yar shekara 60, Hajiya Aisha Hassan wadda aka ce an kubutar da ita ne sakamakon kalubalen rashin lafiya da ke barazana ga rayuwa da ta tabarbare a baya-bayan nan.

Sunayen ‘yan uwa 6 da aka saki sune Abubakar Idris Garba wanda shi ne mahaifin ‘ya’yan hudu, matarsa ​​Maryama Abubakar Bobbo da babban dansu, Ibrahim Abubakar Garba mai shekaru 10. Sauran sun hada da Fatima Abubakar Garba ‘yar shekara 7 da Imran Abubakar Garba mai shekaru 5 da karama Zainab Abubakar Garba mai shekara daya da rabi kacal.

Ya zuwa yanzu, mutane 42 da abin ya shafa sun sake shakar iskar ‘yanci

Alfijr Labarai

Adadin wadanda har yanzu ake garkuwa da su ya kai 35.

A ranar 28 ga watan Maris ne ‘yan bindiga suka tarwatsa titin jirgin, inda suka kashe wasu tare da yin awon gaba da fasinjoji da dama, lamarin da ya bukaci a nuna matukar damuwa game da tsaron lafiyar jiragen kasar.

Slide Up
x