Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa Ta Dakile Yunkurin Yin Garkuwa Da wani Bako

Alfijr Labarai

Alfijr ta rawaito rundunar ƴan Sandan jihar Jigawa, ta dakile yunkurin sace wani bature da ke aiki a kamfanin Tumatur da ke karamar hukumar Birniwa.

Alfijr Labarai

Kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Lawan Shiisu Adam ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

A cewarsa ‘yan bindigar da yawansu ya kai kusan 20 masu tuka babura sun kai hari kan kamfanin Sonia Food Tomatoes a garin Birniwa a kokarinsu na yin garkuwa da Baturen.

Litinin 8/8/2022 da safiyar ranar  wasu ‘yan bindiga kimanin ashirin (20) a kan babura sun kai hari a kamfanin Sonia Food Tomatoes, da ke karamar hukumar Birniwa, da nufin yin awon gaba da wasu fararen fata dake cikin kamfanin,” inji shi.

Alfijr Labarai

Ya bayyana cewa masu garkuwar sun fara harbe-harbe a kai a kai inda suka yi musayar wuta da jami’an ‘yan sanda da ke bakin aiki, inda suka yi nasarar dakile garkuwar tare da garzaya da su cikin daji.

  Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa babu wani da ka yi garkuwa da shi a kamfanin kuma babu wani ma’aikaci ko jami’in da ya samu rauni.

Ya ce an dawo da zaman lafiya a yankin kuma an tsaurara tsauraran matakan dakile hare-haren.

Alfijr Labarai

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, CP Aliyu Sale Tafida ya yabawa jami’an da suka yi gaggawar daukar matakin, ya  kuma bukaci jama’a da su rika baiwa ‘yan sanda damar samun bayanai cikin gaggawa a lokacin da ya dace.

Slide Up
x