Da Ɗumi Ɗuminsa! Gwamnatin Kano Na Shirin Gudanar Da Auren Zawarawa! Inji Dr Zahra’u

Alfijr

Alfijr ta rawaito, kwamishiniyar kula da harkokin mata ta Jihar Kano, Dakta Zahra’u Muhammad ta cewa tuni shirye-shirye sun yi nisa wajen gudanar da shirin nan ba da daɗewa ba, ta karkashin ma’aikatar kula da mata

Alfijr

Dakta Zahra’u ta baiyana hakan ne a wata sanarwar da

Kakakin Yaɗa Labaran jukumar Bahijja Malam Kabara ta bayyana haka a yau Lahadi 27/02/2022

Dakta ta bayyana hakan ne a yayin wani taron daurin aure na mutane 31 maza da mata, wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha a yau Lahadi, Ta ƙara da cewa kuma za ta zaɓi marayu da marasa galihu a sanya su a cikin shirin don faranta musu.

Alfijr

Ta ƙara da cewar, matsalar tattalin arziki, sakamakon annobar korona na ɗaya da ga cikin manyan ƙalubalen da su ka sanya a ka samu tsaiko a shirin auren zawarawa da ƴan mata da Gwamnatin Kano ta saba yi lokaci zuwa lokaci.

Ta kuma kira ga ma’aurata da su yi biyayya ga juna, kuma su bi ka’idojin aure kamar yadda Musulunci ya shar a ta.

Alfijr

Daga Karshe Dakta Zahra’u ta yaba da ƙoƙarin Gidauniyar FOMWAN da DARUL ARQAM da su ka shirya taron.

Ta yi kira ga sauran kungiyoyi masu zaman kansu da su yi koyi da wannan kyakkyawan aikin alheri .