Da Ɗumi Ɗuminsa! Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Khalifa bin Zayed ya rasu a ABU DHABI

Alfijr

Alfijr ta rawaito shugaban hadaddiyar daular larabawa Sheikh Khalifa Bin Zayed Al Nahyan ya rasu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasar WAM ya ruwaito a ranar Juma’a.

Khalifa wanda aka haifa a shekarar 1948, ya hau karagar mulki a shekara ta 2004 a masarautar Abu Dhabi kuma ya zama shugaban kasa.

Ya kuma kasance mai mulkin masarautar Abu Dhabi.

Ana sa ran yarima mai jiran gado Sheikh Mohammed bin Zayed al-Nahyan zai gaje shi a matsayin sarkin Abu Dhabi.

Alfijr

A karkashin kundin tsarin mulkin, mataimakin shugaban kasa kuma firaministan kasar Sheikh Mohammed bin Rashid al-Maktoum, mai mulkin Dubai, zai kasance a matsayin shugaban kasa har sai majalisar tarayya da ta hada da sarakunan masarautun bakwai za su hadu a cikin kwanaki 30 domin zaben sabon shugaban kasa.

Slide Up
x