DA Ɗumi Ɗuminsa! ‘Yan Bindiga Sun Hana Jirgin Sama Tashi, Sun Kuma Kashe Ma’aikaci Daya A Kaduna

Alfijr ta rawaito Rikicin filin jirgin sama na Kaduna ya barke yayin da ‘yan bindiga suka hana jirgin sama tashi kuma sun kashe ma’aikaci daya.

‘Yan bindiga sun hana wani jirgin AZMAN da ke shirin zuwa Lagos tashi ranar Asabar daga filin jirgin Kaduna.

Wata majiya ta tabbatarwa da Solacebase cewa ‘yan bindigar sun harbe ma’aikatan NAMA ne a kusa da titin jirgin da ke filin jirgin.

Majiyar ta ce jirgin na AZMAN bai iya tashi da misalin karfe 12:30 na dare ba saboda kasancewar ‘yan fashin a titin filin jirgin.

Alfijr

“Kamar yadda nake magana da ku a yanzu, akwai sojoji da dama don karfafa tsaro, kodayake yawancin ma’aikatan na fargabar kashe ma’aikatan NAMA, in ji majiyar.

Majiyar ta ce sama da manyan motocin sojoji 10 ne ke filin jirgin a halin yanzu domin karfafawa.

Kamar yadda jaridar Solacebase ta wallafa

Slide Up
x