Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sauke shugaban hukumar alhazai ta Najeriya bayan koke-koke kan yadda aikin hajjin 2024 ya gudana
Hukumomi a Najeriya na dab da sakar wa kamfanoni masu zaman kansu da kuma hukumomi a jihohi gudanar da jigilar aikin Hajji da Umara baki ɗaya.
An ɗauki matakin ne bayan wani taro da kamfanonin gudanar da aikin Hajjin da masu zaman kansu suka gudanar a Abuja, wanda suke son hukumar aikin Hajji ta Najeriya ta bar musu aikin tafiyar da Hajji baki ɗaya daga 2025.
Taron wanda kungiyar kamfanonin aikin Hajji da Umraa masu zaman kansu ta Auhun ta gudanar a Abuja, ya fara ne da duba nasarolri da kuma kurakuran da aka samu a ibadar 2024.
Sannan ya tattauna kan yadda za a tabbatar da cewa su ne suka gudanar da aikin na 2025 baki ɗaya, kamar yadda suka gudanar da wani ɓangare na 2024.
Ikirama Muhammad shi ne mataimakin shugaban ƙungiyar ta Auhun kuma ya faɗa wa BBC cewar suna da ƙwarin gwiwar za su inganta aikin.
A ranar 19 ga wannan watan Agusta ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sauke shugaban hukumar alhazai ta kasa, Jalal Arabi, yayin da hukumar EFCC ke tuhumar sa da yin almundahanar kuɗaɗen aikin Hajjin da ta gabata.
Tinubu ya maye gurbinsa da Farfesa Abdullahi Saleh Usman.
BBC
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj