Dalibai Sun Tare Filin Jirgin Saman Lagos Ba shiga Ba Fita, Saboda Yajin Aikin ASUU


 

Alfijr ta rawaito jagoranci dalibai, ƙarƙashin ƙungiyar dalibai ta kasa, NANS, ta rufe hanyoyin da ke zuwa filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja a jihar Lagos

Alfijr Labarai

Lamarin zanga-zangar wani mataki ne na nuna adawa da matakin yajin aiki da kungiyar malaman jami’o’i ke yi, yadda shuwagabanni suka ki maida kai wajen satin dai daito

Daliban sun fito duk da yanayi ruwan sama da ake kamar da bakin kwarya,an sun  jure sun fito, inda su ka haifar da cunkoson ababen-hawa a titin da ke kan hanyar zuwa filin jirgin, lamarin da ya sa matafiya da dama suka makale.

Lamarin ya faru ne a ifom jami’an rundunar ƴan sandan jihar Legas, da jami’an RRS, da na ‘yan sandan filin jirgin saman Legas, da sauran jami’an tsaro suna nan suna kallon ikon Allah

Alfijr Labarai

Ɗaliban da suka gudanar da zanga-zangar na dauke da alluna da kwalaye, su na ta rera wakokin gwagwarmaya domin nuna rashin jin dadinsu kan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka.

The Nation

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *