Alfijr ta rawaito Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa kafin a kashe Ummita sai da ta kira shi ta sanar da shi cewa iyayenta sun ‘ki amincewa da batun aurenta da d’an China duk da cewar ya musulunta ta sanadin son aurenta da yake yi.
Alfijr Labarai
A cewar Malam sun shafe minti goma sha biyar suna tattaunawa maganganu kan kamarin
Wanda ya ce mata iyayenta suna da gaskiya, sai dai ya kafa mata wasu sharudda guda biyar wadanda idan aka cika su za a iya yin auren
Malamin ya yi alkawarin yin magana da iyayenta don shawo kansu su amince da batun auren nata da ɗan Chana.
Alfijr Labarai
Ranar alhamis da dare ne dai ɗan Chana ya kutsa kai gidansu Ummita da ke unguwar Janbulo ya sossoka mata wuka a wuya, wanda hakan ya yi sanadin ajalinta, sai dai jami’an tsaro sun tabbatar da cafke mutumin domin gurfanar da shi a Kotu don ya girbi abin da ya shuka.