Kotu Ta Ci Tarar Abduljabbar Naira Miliyan goma 10

Daga Rabiu Usman

Alfijr ta rawaito wata babbar kotun tarayya da ke Abuja, a yau Litinin, ta ci tarar Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da ke tsare, Naira Miliyan 10 bisa shigar da kara kan tabbatar da hakkinsa na ɗan ƙasa, inda kotun ta ce hakan rashin ɗa’a ne ga kotun.

Alfijr Labarai

Mai shari’a Emeka Nwite, a cikin hukuncin da ya yanke, ya bayar da umarnin a biya wadanda ake kara kudaden; da su ka haɗa da Kotun Shari’a ta Kofa Kudu, Kano, da gwamnatin jihar Kano a matsayin waɗanda a ke kara na daya da na biyu.

Mai shari’a Nwite ya kuma baiwa Kabara da lauyansa Shehu Dalhatu umarnin su biya gwamnatin jihar Naira dubu 100.

Alƙalin kotun ya ce da zarar kotu ta gamsu cewa an saɓawa tsare-tsaren kotu wajen shigar da ƙara, to kotu na da hakkin hukunta wanda ya shigar da karar.

Alfijr Labarai

Ya ce matakin da lauyan Kabara ya dauka na da nufin samun hukuncin da ya dace ko ta halin kaka.

Nwite ya ce shigar da kara a cikin wata kara mai lamba: FHC/KN/CS/185/2022 a Kano da kuma zuwa Abuja don shigar da ita dai wannan ƙarar mai lamba: FHC/ABJ/CS/1201/2022 kan wannan batu da lauyan ya yi abin alla-wadai ne.

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *