Dubun Wani Mai Unguwa Da Ke Siyar Da Ruwan Rijiyar Al’umma Ta Cika A Kano

Alfijr ta rawaito ana zargin Mai-unguwar Kuwet da ke yankin Rimin Kebe, Ƙaramar Hukumar Ungoggo a jihar Kano da kaifin sayar da ruwan rijiyar al’ummar yankinsa ba da yardarsu ba.

Alfijr Labarai

Bincike ya tabbatar da wata gidauniya ce, mai suna Widi Jalo Foundation ta gina rijiyar ta burtsatse a unguwar bisa roƙon al’ummar yankin suka yi na a kawo musu daukin wahalar ruwa da ke uzzura musu.

Tuni dai wannan kungiyar mai suna a sama ta karbi kokensu, bayan an gina rijiyar ne, sai a ka gano Mai-unguwar yankin, Alhaji Nuhu Muhammad na sayar da ruwan, maimakon al’umma su amfana a kyauta kamar yadda gidauniyar ta umarci al ummar.

Yahaya Sufi Abbas, wanda shine a mazaunin wakilin kungiyar, ya ce sun samu ƙorafe ƙorafen cewa Mai unguwar na sayar da ruwan, ba su yi ƙasa a guiwa ba, su ka yi masa gargadin ya daina.

Alfijr Labarai

Ya kara da cewa, ko da a lokacin ginin rijiyar, sai da dagacin yankin ya bada shawarar cewa, a riƙa sayar da kan famfo ɗaya domin a samu kuɗin da za a riƙa gyaran rijiyar idan ta lalace.

Shi kuma Mai-unguwar kawai sai ya ke sayar da duka kan famfunan, an kuma yi masa magana ya ce wai ba zai daina ba sai dai a kai shi duk inda za a kai shi.

“Mu dai mun faɗa masa cewa za mu danƙa rijiyar ga hannun hukuma kawai tunda dai mu fisabilillahi mu ka gina rijiyar nan domin taimakawa mutanen unguwar kamar yadda su ka nema daga gare mu,” in ji Abbas.

Alfijr Labarai

Da a ka tuntuɓi Mai unguwar, ya ce ya yanke shawarar sayar da ruwan ne domin a samu kuɗin gyaran rijiyar idan ta lalace.

Ya kuma ce tunda haka ta faru, to zai kulle rijiyar gaba ɗaya kuma zai gina wata da kansa, ya kuma ƙara da cewa dama ba wai don bukatar kansa ya ke sayar da ruwan ba sai dan a samu na gyaran rijiyar idan ta lalace.

Sai dai kuma al’ummar yankin na kira ga hukumomi da su kawo musu ɗauki don ganin an yi maslaha don su ci gaba da amfanar rijiyar
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Daily Nigerian

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *