Dubun Wasu Da Suka Kashe Jami’in Vigilante Da Matarsa Da Ɗansa Ta Cika A Kano

Daga
Rabiu Usman

Alfijr ta rawaito Rundunar yan Sintiri ta Vigilantee ta jihar kano ta bayyana samun nasarar kama wasu daga Cikin mutanen da suka kashe guda gada Jami’an Vigilantee na garin Gomo a Karamar Hukumar Sumaila, Isma’il wanda ake kira Ilu Baushe da Dansa da matar Dansa.

Alfijr Labarai

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin babban Kwamandan yan Sintiri na Vigilantee na jihar kano Alhaji Shehu Muhammad Rabi’u yayin Ganawar sa da Wakilin Alfijr a babbar shalkwatar vigilantee dake zaune a hotoro Kano da yammacin wannan ranar Alhamis.

Ya ƙara da cewar, daga cikin manyan aikace aikacen da rundunar tayi a Wannan watan sun hadar da, Kama barayin waya da masu kwacen Babura harma da masu haura gidajen mutane idan Dare yayi, kimanin mutane 70 zuwa 80.

Ya kara da cewa, yanzu lokacin Sanyi, sunyi shiri na musamman domin tunkarar masu labewa suna shiga gidan mutane idan dare yayi.

Alfijr Labarai

A karshe yace dukkannin wadanda rundnar ta Kama sun mika su hannun Jami’an yan sanda domin fadada Bincike.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *